✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta tsare shugaban kungiyar ’yan jarida a kurkuku

Kotun na neman sabbin shugabannin kungiyar kan yi mata tsaurin ido.

Kotu ta ba da umarnin a damko mata tare da tsare shugabannin Kungiyar ’Yan Jarida ta Kasa (NUJ) saboda saba wa umarninta.

Wadanda kotun ta sa a kamo sun hada da Shugaban Kungiyar ta Kasa, Chris Isiguzo, da Sakataren Kungiyar Leman Shuaib da kuma wani jigo a kungiyar mai suna Wuson Bako da sauran ’yan kungiyar da suke ikirarin lashe zaben da ta gudanar a ranar 3 ga watan Yuli, 2021.

  1. SEMA ta tallafa wa mutum 150 a Nguru
  2. Gwamnati za ta tallafa wa Almajirai 12,000 a Yobe

Kotun Kula da Dabi’un Ma’aikata ta Kasa da ke Makurdi, Jihar Binuwai ce ta bayar da umarnin yayin sauraron karar da daya daga cikin ’ya’yan kungiyar, mai suna Dura ya shigar.

Mai shigar da karar yana neman kotun da ta duba ta kuma bayyana ko kungiyar tana da ikon wankewa domin tsayawa takara ga mutumin da bai cika ka’idar yin hakan ba kamar yanda dokar kungiyar ta tanadar.

A kan haka ne kotun ta dakatar da zaben da kungiyar ta NUJ ta gudanar bisa karar da shi wannan Dura ya shigar har sai an cimma matsaya.

A yayin sauraron ci gaban shari’ar, kotun ta wanke Shugaban Rikon  Kungiyar, Kajo Martins, saboda biyayyarsa ga umarninta na kaurace wa zaben.

Alkalin kotun, Mai Shari’a I.J. Essien, ya bayyana cewa Bemdoo Ugber, wanda ke ikirarin lashen zaben Shugaban Kungiyar da cewa, “Kai shugaba ne ba bisa ka’ida ba; Me za ka ce wa kotu bayan ka yi buris da kiran da ta yi maka a matsayinka na mai amsa kara? Yau daga nan gidan kurkuku za a tafi da kai”.

Alkalin ya kara da cewa, “Ta yaya  za a samu ci gaba a wannan halin na rashin tsaro idan har wasu mutane suna goyon tayar da zaune tsaye? Duk wadanda aka ce sun ci zaben an yanke musu hukuncin zaman gidan kurkuku har zuwa zama na gaba”.

Alkalin ya kuma umarci wanda ake kara, mutanensa da su daina daukar kansu a matsayin shugabannin NUJ a Jihar Binuwai, sannan su dawo da duk kayayyakin kuniygar da ke hannunsu, su damka a hannun shugaban kungiyar na rikon kwarya, Steven Ijoh.