✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta yanke wa budurwa hukuncin kisa ta hanyar rataya a Kano

An sami matar ne da laifin kashe makwabciyarta, saboda ta kira ta da karuwa

Wata Babbar Kotun Jihar Kano da ke zamanta a Miller Road, a ranar Laraba ta yanke wa wata budurwa hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samunta da laifin kashe makwabciyarta.

Kotun, karkashin Mai Shari’a Amina Adamu, ta yanke wa budurwar mai suna Aisha Kabir hukuncin ne bayan shafe sama da shekara guda ana gudanar da shari’arta.

An gurfanar da Aisha ne bisa zargin kashe Bahijja ta hanyar soka mata wuka a wuya bayan wani sabani da ya faru tsakanin su.

Rikicin ya samo asali ne yayin da A’isha ta kira Bahijja da sunan karuwa, wanda ya kai ga rigima tsakaninsu har Bahijja ta rasa ranta sakamakon wuka da A’isha ta soka mata.

A zaman kotun na ranar Laraba, Alkalin ta ce ta samu wadda ake zargin da laifi kuma ta yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Sai dai da yake tsokaci bayan yanke hukuncin, lauyan da ke kare wadda ake tuhuma, Barista Auwal Abubakar Ringim ya ce ba za su ce komai ba dangane da yunkurin daukaka kara har sai sun zauna sunyi nazari.

‘“Abin da ya faru shi ne an samu sabani da ita wadda ta rasu da kuma wadda aka yanke wa hukunci, daga baya ita wadda ta rasu da kawayenta suka je har wajen aikin wadda aka yankewa hukuncin suka fara dukanta, sannan fada ya barke a tsakaninsu, a nan ne abun ya faru,” inji Barista Ringim.

An nasu bangaren, dan uwan wacce aka kashe din mai suna Danlami Abbas ya bayyana farin cikinsa da hukuncin da babbar kotun ya yanke wa wadda ake tuhumar.

Shi ma lauyan gwamnati, Barista Lamido Abba Sorondinki ya bayyana gamsuwarsu da wannan hukunci da kotun ta yanke.

Ya kuma ce suna jiran wadanda akai kara idan sun daukaka kara.