✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotun Koli ta tabbatar da hukuncin soke rijistar jam’iyyu 74

Kotun Kolin ta ce matakin ya yi daidai tanade-tanaden Kundin Dokar Zabe ta Kasa.

Kotun Kolin Najeriya a ranar Juma’a ta tabbatar da hukuncin Kotun Dukaka Kara da ya soke rijistar jam’iyyun Najeriya 74.

A shekarar 2020 ne dai Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta ta sanar da soke rijistar jam’iyyun saboda gazawarsu wajen lashe ko da kujera daya yayin babban zaben shekarar 2019.

Da take yanke hukunci wanda Mai Shari’a China Nweze ya jagoranta, Kotun Kolin a ranar Juma’a ta ce matakin ya yi daidai tanade-tanaden Kundin Dokar Zabe ta Kasa.

Tun da farko dai jam’iyyar NUP ce ta daukaka karar tana kalubalantar dakatarwar da INEC ta yi mata cewa ba ya kan ka’ida.

Tun da farko dai sai da jam’iyyar ta fara zuwa Babbar Kotun Tarayya da kuma Kotun Daukaka Kara amma duka suka yi fatali da bukatarta.

A ranar 29 ga watan Yulin 2020 ne dai Kotun Daukaka Kara dake zamanta a Abuja ta tabbatar da cewa INEC na da ikon soke rijistar jam’iyyun.

A lokacin dai INEC ta ce ta dauki matakin ne a watan Fabrairun bara saboda sun gaza cimma mafi karancin bukatar da ake yi wa kowacce jam’iyya.