Kungiyar daliban manyan makarantun Najeriya ta yi barazanar kawo cikas a zaben fidda gwani da jam’iyyar APC da PDP za su gudanar idan har ba a bude jami’o’o’in kasar nan ba.
Gabanin zaben shekarar 2023, harkokin siyasa sun kan kama a Najeriya, inda jam’iyyun siyasa ke shirin gudanar da zabukan fidda ‘yan takara a matakai daban-daban a watan Mayu, 2022.
- Rasha ta harba makami mai linzami a filin jirgin saman Ukraine
- Raba kafa: Bala Mohammed ya sayi fom din takarar Gwamnan Bauchi a ‘boye’
Sai dai a wata sanarwa daga hannun shugaban kungiyar daliban, Sunday Asefon, kungiyar ta caccaki shirye-shiryen da ‘yan siyasa ke yi na samun tikitin tsayawa takara a yayin da jami’o’in kasar nan ke garkame tsawon kusan watanni uku sakamakon yajin aikin da ASUU ta tsunduma.
Shugaban, ya bayyana ‘yan siyasar Najeriya a matsayin miyagu masu son zuciya, marasa tausayi.
An jima ana kai ruwa rana tsakanin ASUU da gwamnatin tarayya kan batun cika mata wasu alkawuran da ta dauka mata, lamarin da ya sanya malaman jami’o’in tsunduma yajin aiki a lokuta mabambamta.