✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Kungiyar lauyoyi ta yi ragon azancin soke gayyatar El-Rufa’i’

Tsohon Sarkin Kano kuma tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Muhammadu Sanusi II ya soki Kungiyar Lauyoyi ta Kasa (NBA) kan janye gayyatar da ta…

Tsohon Sarkin Kano kuma tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Muhammadu Sanusi II ya soki Kungiyar Lauyoyi ta Kasa (NBA) kan janye gayyatar da ta yi wa Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufa’i zuwa babban taronta da ke tafe.

Sanusi wanda ke ziyarar aiki ta mako guda a Kaduna, ya ce kungiyar ba ta da wata kwakkwarar hujja kan zarge-zargen da take wa gwamnan.

“Idan ka ce wani ba ya girmama doka to sai ka fadi ta yaya? Idan ka ce wani bai yi abin da ya dace ba a yanayin magance rikici, sai ka yi bayanin yadda ya yi hakan. Kowa zai iya cewa komai, zan iya zargin ka da rashawa, amma hakan ba ya nufin komai”, inji Sanusi.

A ziyarar tasa ta farko tun bayan da ya koma Legas da zama bayan tubeshi daga sarauta, tsohon sarkin wanda ke jawabi a Gidan Gwamnatin Jihar Kaduna, ya ce ko da dai bai so ya tsoma bakinsa a kan rikicin ba, musamman kasancewar ’yan Najeriya da dama sun bayyana ra’ayoyinsu a kai, kamata ya yi lauyoyin su bar shi ya kare kansa a maimakon soke gayyatar tasa.

“Tunda kun fada masa abin da kuka ce yana yi ba daidai ba, ke nan zai iya koyar wani abu daga wajenku da kun barshi ya zo. Amma soke gayyatarsa bai dace da tunanin masu son ci gaban kasa ba,” inji Sanusi.

Aminin na El-Rufa’i ya ce a matsalar tsaron yankin Kudancin Kaduna ta dade kuma gwamnan na yin bakin kokarinsa wajen ganin ya kawo karshenta.

Ya ce,“Yankin Arewa gaba dayansa na fama da kalubale iri-iri saboda akwai masu samun biyan bukata daga matsalar tsaro.

“Muna fama da kalubalen rabuwar kai na addini da kabilanci, to idan wani ya nuna sha’awar yin abin da ya dace wasu kuma ba sa bukatar haka, dole a samu tirjiya,” inji Sanusi.