✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar Miyetti Allah ta goyi baya a haramta yawon kiwo

Miyetti Allah ta goyi bayan gwamnonin Kudu cewa a haramta yawon kiwo.

Kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) ta bayyana goyon bayanta ga matsayin gwamnonin Kudu kan haramta yawon kiwo.

Uban kungiyar Miyetti Allah na Kasa, Sanata Walid Jibril ne ya sanar da hakan, yana mai cewa haramta yawon kiwo zai kawo karshen rikicin manoma da makiyaya.

Sanata Walid Jibril wanda shi ne Sarkin Fulanin Nasarawa, ya ce akwai bukatar samar da hanya mafi inganci na yin kiwo, idan aka yi la’akari da matsalolin da kiwon shanu ke haddasawa a kasashen Afirka, musamman ma Najeriya.

A cewarsa, an shafe sama da shekara 100 ana kiwo a nahiyar Afirka ba tare la’akari da bukatar a samar da kyakkyawan yanayin yi kiwo-sake ko samar da gandun kiwo ba.

Ya ce hakan ta faru ne saboda a shekarun baya makiyaya da dabbobin su da ma manoma ba su da yawa sosai, musamman a Najeriya.

Uban na Miyetti Allah ya jaddada cewa amma a halin yanzu yawan al’umma ya karu ga kuma fasahar noma da ke iya cin wuri mai fadin gaske, don haka akwai bukatar sauya zamantar da harkar kiwo.