✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwastam ta kama mota makare da makamai

An boye makaman ne cikin garin alabo da shinkafa ’yar gwamnati.

Jami’an hukumar kwastam sun kama albarusai 751 a cikin wata mota da ake boye a cikin garin alabo.

An kama motar ce a yayin wani sintiri da jami’an hukumar suka gudanar a yankin Igbo-Ora na Jihar Oyo.

Kwanturolan Hukumar Kwastam da ke kula da yankin, Hussein Kehinde Ejibunu, ya ce, “A cikin kayan da aka kama akwai harsasai 751 masu tsawon 70mm, akwai kuma bahunan rogo da shinkafa ’yar gwamnati.

“Motocin da kama da kayan a ciki na tsare a hedikwatarmu domin a kara bincike”.

Sai  dai ya ce diraben motar da yaronsa sun tsere ne suka bar moatar a lokacin da suka yi ido hudu da jami’an kwastam din.

Ejibunu ya kuma yi kira ga jama’a da su rika taimaka wa hukumar da bayanai domin yakar ayyukan masu fasakwauri.