✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lampard ya zama kocin Chelsea

Kulob din Chelsea da ke Ingila a jiya Alhamis ya bayar da sanarwar daukar Frank Lampard a matsayin sabon kocin kulob din. Frank Lampard dan…

Kulob din Chelsea da ke Ingila a jiya Alhamis ya bayar da sanarwar daukar Frank Lampard a matsayin sabon kocin kulob din.

Frank Lampard dan shekara 41 ya samu nasarori masu yawa a lokacin da yake yi wa Chlsea kwallo.  Hasalima shi ne dan kwallon da ya fi yawan zura kwallaye inda kafin ya bar kulob din ya zura kwallaye 211 kuma har yanzu babu wanda ya kama kafarsa.

Kafin yanzu, Lampard shi ne kocin kulob din Derby County da ke wasa a rukunin ’yan dagaji a Ingila.

Kamar yadda rahoton ya nuna, Lampard ya sanya hannu ne a kwantaragin shekara uku kuma ya maye gurbin tsohon koci Maurizio Sarri dan asalin Italiya wanda ya koma kulob din Jubentus na Italiya a watan jiya.