✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Luguden wuta ya sa ’yan bindiga sun fara neman sulhu a Zamfara – Matawalle

A maimakon haka, ya ce ruwan wuta za a ci gaba da yi musu har sai an ga bayansu.

Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle ya ce luguden wutar da sojoji ke yi a kan ’yan bindiga a Jihar ya sa sun fara neman a yi sulhu.

Sai dai ya ce Gwamnatin Jihar ba za ta sake amincewa da yin wani sulhu da su ba kasancewar a baya sun sha karya yarjejeniyar neman yin hakan.

Da yake jawabi a Gusau, babban birnin Jihar ranar Asabar, Gwamna Matawalle ya ce a maimakon haka, jami’an tsaro za su ci gaba da yi musu ruwan wuta har sai sun ga bayansu.

“Gwamnatinmu ba za ta sake amincewa da yin sulhu da ’yan bindiga ba saboda a baya sun ki rungumar tayin zaman lafiyar da muka yi musu,” inji Gwamnan.

Daga nan sai ya yi kira ga jama’a da su kara hakuri kuma su goyi bayan sabbin matakan tsaron da aka bullo da su a Jihar na fatattakar ’yan bundigar da masu hada hannu da su.

Gwamnan ya kuma ce yanzu haka wasu, daga cikinsu sun fara guduwa zuwa wasu Jihohin saboda zafin hare-haren.

Ya kuma gargadi ’yan siyasa kan su ji tsoron Allah su daina tallafa wa ’yan bindigar ta kowacce fuska, “musamman ta hanyar raba wa mutane babura wadanda su kuma daga karshe suke sayarwa da ’yan bindigar don ci gaba da mummunan aikinsu.”

Ya sha alwashin gurfanar da duk dan siyasar da aka samu da hannu a ciki a gaban kotu.

Yanzu haka dai, katse hanyoyin sadarwar da aka yi na tsawon mako biyu ya janyo rufe kusan ilahirin harkokin kasuwanci a Jihar.

Kusan dukkan bankuna da harkokin wayoyin salula da na intanet da sauran makamantansu an dakatar da hada-hadarsu.