✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lukaku zai goya lamba 9 a Chelsea

Rahotanni daga birnin Landan sun tabbatar da cewa, sabon dan wasan da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta dauko daga Inter Milan, Romelu Lukaku, zai…

Rahotanni daga birnin Landan sun tabbatar da cewa, sabon dan wasan da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta dauko daga Inter Milan, Romelu Lukaku, zai goya lamba 9 a kungiyar.

Lukaku bayan sake dawowarsa kungiyar, ya karbi lamba 18 amma daga bisani ya karbi lamba 9 wacce Tammy Abraham yake goyawa kafin komawarsa AS Roma a bazarar nan.

Chelsea dai ta cefanar da ’yan wasanta biyu da ke buga mata lamba 9 da suka hada Oliver Giroud wanda ya koma AC Milan da kuma Tammy Abraham da ya tafi Roma.

Abraham ya kulla yarjejeniyar shekaru biyar da AS Roma wacce a yanzu tsohon kocin Chelsea, Jose Mourinho ne yake jagorantarta.

Shi dai Romelu Lukaku ya ce ya sake koma wa Stamford Bridge a matakin kwararren dan wasa tun bayan kaka biyu rabonsa da Firimiyar ta Ingila.

Dan wasan shekara 28 ya koma Chelsea daga Inter Milan a makon jiya kan fam miliyan 97.5 a karo na biyu da zai buga mata tamaula, bayan zaman da ya yi tsakanin 2011 zuwa 2014.

“Yanzu ne nake cikakken dan kwallo. Na tanadi dukkan kwarewar da mai cin kwallaye ke bukata a wasanni, zan kuma kara kwazo a fannin da nake da rauni,” a cewar Lukaku.

Lukaku shi ne dan wasan da Chelsea ta saya mafi tsada a tarihi, kuma na biyu a tsada a Birtaniya, bayan Jack Grealish da Manchester City ta dauka daga Aston Villa a bana.

Dan wasan na tawagar Belgium shi ne kan gaba a ci wa Inter kwallaye inda ya zura kwallaye 24 a gasar Serie A ta kakar da ta gabata.

Lukaku ya taimaka wa kungiyar lashe kofin Serie A a karon farko cikin shekara 11.

Bayan da ya bar Stamford Bridge, Lukaku ya buga wasannin aro a Everton daga nan kungiyar ta saye shi, ya koma Manchester United a 2017.

Dan kwallon ya yi kaka biyu a United duk da magoya bayan kungiyar sun nuna masa rashin kauna da cewar ya yi nauyi kuma bai da kuzari.

Lukaku bai buga wa Chelsea karawar da ta doke Crystal Palace 3-0 ranar Asabar a wasan makon farko a gasar Premier.

Ana sa ran zai fara buga wa Chelsea wasa a karawar da za ta yi da Arsenal ranar Lahadi.

Chelsea ta taba bayar da aron Abraham zuwa kungiyoyin Bristol City, Swansea City da kuma Aston Villa.

Tuni dai kungiyar da Lukaku ya baro wato Inter Milan ta maye gurbinsa da Edin Dzeko wanda ta siyo daga Roma.