✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Magidanci ya nemi a raba aurensu saboda fitinar matarsa

Ya ce ya gaji da fitinar matar tasa shi ya sa ya nemi kotu ta raba aurensu

Wani magidanci ya maka mai dakinsa a kotu a Ilori, babban birnin Jihar Kwara, yana mai neman a raba aurensu saboda ya gaji da fitinarta.

Haka nan, ya nemi kotu ta mika masa ragamar kula da ‘ya’yansu bayan raba auren.

Lauyan matar, Maruf Ibrahim, ya fada wa kotun cewa wadda yake karewa ta amince a raba auren nasu amma ba a kan zargin da maiginta ya yi ba.

Ya ce babu inda wadda yake karewa ta zama mai rashin biyayya ga mijinta balle ta fitine shi.

Daga nan, ya bukaci kotun da ta mika ragamar kula da yaran a hannun mahaifiyarsu saboda a cewarsa yaran kanana ne.

Ya kuma nemi kotu ta dora wa mahaifin nauyin dawainiyar yaran da kuma kudin makarantarsu da sauran hidima.

Alkalin kotun, AbdulQadir Ibrahim, ya buakci mai kara da ya gabatar da hujjoji da shaidun da za su nuna ya cancanci rike yaran

Daga nan, ya dage karar zuwa 20 ga watan Maris.