✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mahaifiyar Sarkin Bwari ta rasu

Mahaifiyar Sarkin Bwari ta rasu ana tsaka da shirye-shiryen bikin ba shi sandar sarauta

Allah Ya yi wa mahaifiyar Sarkin Bwari, Alhaji Auwal Musa Ijakoro, rasuwa a safiyar Alhamis.

Mahaifiyar sarkin mai suna Hajiya Hauwa Musa Ijakoro ta rasu tana da shekaru 69 a duniya.

Fadar Sarkin Bwari ta sanar cewa za a gudanar da jana’izar Hajiya Hauwa Musa Ijakoro da misalin karfe 12 na rana.

Allah Ya yi mata rasuwa ne bayan ta yi fama da rashin lafiya, a asibitin Nizamiyye da ke Abuja.

Rasuwar mahaifiyar sarkin na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirye-shiryen bikin mika masa sandar sarauta.

A ranar Asabar 27 ga watan Agusta da muke ciki ne za a yi bikin mika wa Alhaji Auwal Musa Ijakoro sandar a matsayin Sarkin Bwari.