✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun kashe ’yan banga 19 a kauyen Sakkwato

Maharan sun kai farmaki da nufin kashe shugaban ’yan bangar.

’Yan banga 19 sun rasu a yayin da ’yan bindiga suka kai hari kauyen Yartsakuwa na Karamar Hukumar Rabah a Jihar Sakkwato.

Wani mazaunin kauyen da ya tattauna da Aminiya ta wayar tarho, ya ce ’yan bindigar sun kashe ’yan bangar ne a yayin da suka yi kokarin dakile harin ’yan bindigar.

“Sun zo da shirin kashe shugaban ’yan bangar kauyen nan,” cewar mazaunin kauyen wanda ya ce maharan sun shiga kauyen ne da misalin karfe 1 na daren Litinin.

Rahotanni sun ce an kashe shugaban ’yan bangar, wanda aka boye sunansa ne a gonarsa.

Da yake tabbatar da faruwar harin, Kansilan Gundumar Ghandi “A”, Aminu Mu’azu Ghandi, ya ce an kashe ’yan banga 14 tare da wasu mutum biyar, sannan wasu mutum biyar da suka samu rauni an kai su asibiti don ba su kulawa.

Kansilan ya kara da cewa maharan sun sace dabobbi da dama a yankin.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin ’yan sandan Jihar Sakkwato, ASP Sanusi Abubakar, ya ce ’yan banga 10 ne suka rasa rayukansu ba 14 ba.

Ya shawarci ’yan banga a jihar da su rika jinkirta wa jami’an tsaro su iso kafin su afka wa ’yan bindiga a duk lokacin da suka kawo hari.