Mahara sun yi garkuwa da Hakimin MaFarang a Karamar Hukumar  Mayobelwa na Jihar Adamawa, Ardo Mustapha Ardo Ahmadu.

Maharan dauke da muggan makamai sun yi dirar mikiya ne a gidan Ardo Mustapha wanda shi ne Sarkin Noma Adamawa, suka dauke shi a cikin tsakar daren Talata.

Wani mazaunin yankin ya ce maharan sun kutsa gidan ne da misalin karfe 12 na dare, ’yan sa’o’i i bayan dawowar basaraken daga Abuja, suka kuma tafi da shi.

Majiyarmu ta ce karfin makaman maharan da irin luguden wutan da suka rika yi a iska sun tilasta wa ’yan banga masu sintiri a yankin da suka yi yunkurun kai wa basaraken dauki ja da baya.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Adamawa, DSP Sulaiman Nguroje ya tabbatar da rahoton sace basarken, kuma ana kokarin ceto shi daga hannun masu garkuwar.

“Gasakiya ne an yi garkuwa da basaraken da misalin karfe 1200 zuwa 1:00 na dare”, in ji shi.

Ya kuma ce, “an tura jami’an ’yan sanda domin kubtuar da shi da kuma kamo wadanda suka yi garkuwa da shi.

“A shirye Rundunarmu take da ta bayar da tukwici na kudi ga duk wanda zai taimaka da bayanan da za su kai ga cafke wadanda suka suka yi wannan mummunan aiki.”