✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai cikin ’yan biyu ta dauki cikin da na uku kafin ta haihu

Wadansu ma’aurata sun shiga cikin yanayin farin ciki bayan da aka yi wa matar gwajin juna biyu inda ya nuna tana dauke da tagwaye daga…

Wadansu ma’aurata sun shiga cikin yanayin farin ciki bayan da aka yi wa matar gwajin juna biyu inda ya nuna tana dauke da tagwaye daga bisani kuma aka gano ta sake samun wani cikin inda a yanzu take da jarirai uku a cikinta.

Matar wanda ta wallafa karin juna na biyun da take da shi a kafar sadarwar zamani ta TikTok a shafinta na @theblondebunny1, ta sanar da abin mamakin cewa a yanzu tana shirin haifar ’yan uku a bana.

Matar wadda ’yar kasuwa ce ta ce, hakan na faruwa idan mace ta dauki ciki sau biyu a cikin wata guda.

Matar ta ce: “Kamar yadda jikin mace yake samun sauyi da zarar ta samu ciki sai ta daina jinin al’ada yadda ba za ta fitar da wani kwan halitta ba, har sai ta haihu.

“A yanayin da na samu kaina ba haka abin faru da ni ba.

“Kusan kashi 10 cikin 100 na mata za su iya fitar da kwan halitta sau biyu a cikin wata guda. Ina tunanin kashi 3 cikin 100 ne kawai za su sake daukar juna biyu bayan ba su haife na farko ba.”

“A kimiyyance ke nan jariran za su samu bambancin wa’adin haihuwa,
an yi sa’a cewa an samu cikinsu ne kusa da kusa, kuma za a haife su rana guda, duk za a iya kiransu ’yan uku kamar wadanda aka samu
cikinsu lokaci guda,” inji ta.

Ta kara da cewa “A yanzu da ranar kwan halittar ya bambanta da juna biyu na farko da aka samu, za a samu bambancin girma ko habakar halittar da tagwayen farko.

“Nawa cikin bambancin ’yan makonni ne, yayin da na wadansu ake samun bambancin watanni, inda za a iya samun bambancin ranar haihuwa.”

Matar auren wadda ta ce ba a san jinsi jariran da za ta haifa ba, ta ce likitoci sun ce jariri na uku ba zai zama yana da cikakken koshin lafiya ba, kamar sauran ’yan biyun farko da aka fara samun cikinsu.

“Tagwayen farko da aka fara samu, sun girmi na ukun da kwana 11, yadda aka gano cewa an samu cikin na ukun ne daga baya,” inji ta.

“Don tabbatar da cewa, an samu karin wani sabon juna biyu bayan tagwayen da aka fara gwajin cewa suna cikin, sannan aka gano cewa, na ukun da aka samu bai da cikakken koshin lafiya kamar sauran, don haka ake yin hoton cikin duk mako biyu.

“A haka ne dai suke ta girma bayan tagwayen sun girmi na karshen da kwana 11 a cikin mahaifa,” inji ta.

Ta gargadi duk mai juna biyu cewa: “Idan mijin matar da take dauke da juna biyu, yana kwanciyata da ita – zai zamar min wani gargadi.”

Ana sa ran uwar ’yan uku ta haihu a watan Afrilu ko Mayun bana.

Ta ce, ana shirin a haifi duk jariran bayan mako 28, sannan a dauke su don kula da su bayan mako 32 ko 35.

Matar ta ce ita da mijinta sun yi ban-kwana da samun juna biyu, kuma akwai yiwuwar ba za su sake samun ’ya’ya ba.