✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai kwace waya ya guntule yatsun matashi a Abuja

’Yan sanda sun damke wani mai kwacen da ya guntule yatsu biyun wani matashi a garin kwace masa waya a Abuja.

’Yan sanda sun cika hannu da wani mai kwacen waya da ya guntule wa wani matashi yatsu biyun hannunsa a garin kwace masa waya a Abuja.

An cafke mai kwacen wayan ne bayan wannan aika-aka da ya yi wa makiyayin mai shekaru 18 a unguwar Lugbe.

Bayan dawowa daga kiwo ne matashin mai suna Saleh Ibrahim ya je karbo wayoyinsa a wurin masu caji, inda a hanyar dawowa wanda ake zargin ya far masa, ya sare shi a kai.

Kawun Saleh ya ce mai kwacen wayan na neman sake sarar Saleh a kai ne Saleh ya sa hannunsa domin karewa, nan take mai kwacen ya guntule masa yatsu biyu.

A cewarsa, “Sai ya zubar da duk wayoyin biyu don ya ceci rayuwarsa, ya dawo gida, aka kai shi asibiti, yanzu haka an kwantar da shi.

“Mun sanar da ’yan sanda a caji ofis na Tudun-Wada a Lugbe, suka kira ofishin ’yan banga na kauyen Jiddu, suka kamo wanda ake zargin.

Mun nemi karin bayani daga kakakin ’yan sandan Abuja, SP Josephine Adeh, amma ta ce za ta bincika, in ya so daga baya ta yi bayani.