✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa ta tsige Mataimakin Gwamnan Edo

Mataimakin Gwamnan ya yi watsi da damar kare kansa daga zargin da majalisar ke yi masa.

Majalisar Dokokin Jihar Edo ta tsige mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Philip Shaibu.

A safiyar wannan Litinin ’yan majalisar suka tsige Kwamared Shuaibu wanda ya sha fama da takun-saka tsakaninsa da Gwamna Godwin Obaseki.

Bayanai sun ce mataimakin gwamnan ya sha ƙin amsa goron gayyatar kwamitin mutum bakwai da majalisar ta kafa domin binciken zargin da ake yi masa.

Bayan ƙin amsa goron gayyatar ne kwamitin karkashin jagorancin Mai Shari’a S.A Omonu ya gabatar da shawarar sallamar mataimakin gwamnan, la’akari da cewa ya yi watsi da damar kare kansa da majalisar ta ba shi.

A yayin zaman kwamitin na ranar Juma’ar da ta gabata, Mai Shari’a Omonuwa ya yi babatu kan rashin amsa goron gayyatar da mataimakin gwamnan ya yi.