✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Obaseki ya zaɓi ɗan shekara 38 sabon mataimakin gwamnan Edo

An haifi sabon mataimakin gwamnan a ranar 19 ga watan Yulin 1986 a Ƙaramar Hukumar Akoko Edo ta jihar.

Gwamna Godwin Obaseki ya zaɓi Injiya Omobayi Marvellous Godwins mai shekara 38 a matsayin sabon mataimakinsa.

Wannan na zuwa ne bayan tsige Kwamared Philip Shaibu da aka yi a safiyar wannan Litinin ɗin.

Kamar yadda bayanai suka tabbatar, an haifi sabon mataimakin gwamnan a ranar 19 ga watan Yulin 1986 a Ƙaramar Hukumar Akoko Edo ta jihar.

Sabon mataimakin gwamnan ya yi digirinsa na farko a Injiniyan lantarki sai kuma digiri na biyu a fannin kula da gudanar da al’umma a Jami’ar Benin.

Aminiya ta ruwaito cewa an dai tsige Kwamared Philip Shaibu a zaman da Majalisar Dokokin Edo ta yi ranar Litinin a Benin, babban birnin jihar

Tsige Shaibu ya biyo amincewa da wani rahoton kwamitin mutum bakwai da alƙalin alƙalan jihar Daniel Okungbowa ya kafa domin yin bincike kan zarge-zargen aikata ba daidai ba da ake yi wa mataimakin gwamnan.

A makon da ya gabata ne majalisar dokokin jihar ta Edo ta fara shirin tsige Shaibu, inda ’yan majalisa 21 cikin 24 ne suka sa hannu kan takardar ƙorafin.

’Yan majalisar sun zargi Shaibu da yin ƙarya da kuma bayyana sirrikan gwamnatin jihar.

A zaman da ta yi ranar Talatar da ta gabata, shugaban majalisar, Blessing Agbebaku ya shaida wa ’yan majalisar cewa wa’adin kwana bakwai da aka bai wa Shaibu ya mayar da martani ga takardar fara shirin tsige shi ya wuce.

Tsige Shaibu na da nasaba da takun saƙar siyasa da ke tsakaninsa da ubangidansa, Godwin Obaseki.