✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa ta umarci Malami ya dakata da goge sashe na 84(12) daga Dokar Zabe

Majalisa za ta daukaka kara kan hukuncin goge sashe na 84(12) na Dokar Zabe ta 2022.

Majalisar Wakilan Najeriya ta umarci Ministan Shari’a Abubakar Malami da ya dakata da goge sashe na 84(12) na Dokar Zabe ta 2022.

Sashe na 84(12) da ke cikin Dokar Zaben dai ya ce dole ne duk wani mai rike da mukamin gwamnati da ke da sha’awar yin takara a zaben kasar ya sauka daga mukaminsa.

Sai dai umarnin Majalisar na zuwa ne yayin da ta yanke shawarar daukaka kara kan hukuncin da Kotun Tarayya ta yi na bai wa Ministan umarnin goge sashe na 84(12) na Dokar Zabe ta 2022.

A kan haka ne Majalisar ta nemi ministan shari’ar kuma antoni janar da ya dakatar da aiwatar da umarnin har sai an kammala daukaka karar.

Ita ma Majalisar Dattawa ta ce za ta daukaka karar bayan sanatoci da dama sun bijiro da bukatar yin hakan a zamansu na ranar Laraba.

Kakakin Majalisa Femi Gbajabiamila ya koka kan dalilin da ya sa aka kai karar kotun da ke Jihar Abiya a Kudancin Najeriya, yana mai cewa “majalisa ce kadai ke da ikon sauyawa ko yin doka a KundinTsarin Mulkin Najeriya.”

BBC ya ruwaito cewa a zaman da ya gudana a zauren Majalisar Dattawa, an samu ’yar hatsaniya a lokacin da Sanata Sani Musa daga Jihar Neja ya bukaci a cire sunansa daga jerin wadanda suka amince a daukaka karar.

Sanatan da ke wakiltar Mazabar Neja ta Tsakiya na cikin ’yan takarar neman shugabancin jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya a zaben da a gudanar ranar Asabar, 26 ga watan Maris.

A bayan nan ne dai Gwamnatin Tarayya ta ce jami’anta da ke takara ba za su sauka daga mukamansu ba biyo bayan umarnin kotu na soke sashe na 84(12) daga cikin Dokar Zaben.

Mai magana da yawun Ministan Shari’a, Dokta Umar Gwandu ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a Juma’ar makon jiya.

Wannan sanarwar na zuwa ne ’yan sa’o’i bayan da wata kotu da ke zamanta a Umahia, babban birnin Jihar Abia a Kudu maso Gabashin kasar ta umurci Malami da ya cire sashen ba tare da bata lokaci ba.

Gwandu ya ce matakin da ma’aikatar shari’ar ta dauka, biyayya ce ga umarnin da kotu ta bayar.