✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa Ta Yi Barazanar Cefanar Da Hukumar NIPOST

Majalisar Dattawa ta zartare kasafin hukumar saboda rashin samar da kudaden shiga da ya kamata ga gwamnati

Majalisar Dattawa ta yi barazanar cefanar da hukumar kula da gidajen waya ta kasa (NIPOST), saboda rashin samar da kudaden shiga da ya kamata ga Gwamnatin Tarayya.

Shugaban kwamitin harkokin kudi na majalisar, Sanata Sani Musa, shi ne ya yi wannan barazana lokacin sauraron ra’ayoyin jama’a kan yadda gwamnati za ta tsara kashe kudi na matsakaicin zango, daga shekarar 2024 zuwa 2026.

Sanata Sani Musa ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda hukumar ke kasa tara kudin shiga daga harajin kan sarki da take karba.

A saboda haka kwamitin ya bai wa hukumar wa’adin shekara biyu kan ta samar da sabon tsarin dogaro da kanta, daga kudin da take samu, ko kuma ’yan majalisar su cefanar da ita ga ’yan kasuwa.

Sani Musa ya ce bai kamata hukumar ta kara kudin da za ta kashe ba, daga biliyan 13 a shekarar nan zuwa biliyan 18 a shekara ta 2024 mai zuwa.

Duk da yake Sanatar Abuja, Ireta Kingibe, ta yi kokarin kare ayyukan hukumar ta NIPOST, amma takwaranta Osita Izunaso, ya ce bai kamata a ce sauran hukumomi suna samar da kudin shiga, amma NIPOST ta gagara yin haka ba.