✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Dokokin Jihar Neja ta tsige Shugaban Masu Rinjaye

An tsige shi saboda rashin halartar zaman gabatar da Kasafin 2021

A ranar Laraba ne ’yan Majalisar Dokokin Jihar Neja suka tsige Shugaban Masu Rinjaye, Honorabul Abba Bala Mohammed da mataimakiyarsa, Binta Mamman, kan zargin sakaci da aikinsu.

Dan majalisa mai wakiltar Bida 1, Bako Kasim Alfa ne ya gabatar da kudirin tsigewar sannan dan majalisa mai wakiltar Wushishi, Mohammed Lokogoma ya goyi bayan hakan.

Daga bisani ’yan majalisar sun janye kudirin tsige mataimakiyarsa, Binta Mamman, saboda harbuwa da ta yi da cutar coronavirus a baya-bayan nan.

Amma sun tabbatar da cewa ba gudu ba ja da baya dangane da tsige Shugaban Masu Rinjayen, mai wakiltar Borgu.

’Yan majalisar sun koka game da yadda ya ki halartar zaman nazari kan kasafin kudin Jihar na 2021, duk da cewar ya san muhimmancin halartar zaman.