✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda COVID-19 ta yi wa Majalisar Dokokin Neja dirar mikiya

Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Neja, Bawa Wuse da Akawun Majalisar, Mohammed Kagara sun killace kan su bayan kamuwa da COVID-19

Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Neja, Bawa Wuse da Akawun Majalisar, Mohammed Kagara sun killace kan su bayan kamuwa da COVID-19 da ta yi wa majalisar dirar mikiya.

Kwamishinan Watsa Labarai da Tsare-tsare na jihar, Alhaji Mohammed Idris ne ya tabbatar wa manema labarai hakan a Minna ranar Lahadi.

Ko da yake bai bayar da cikakken bayani a kai ba amma ya tabbatar da cewa gaskiya ne.

Kazalika, dan majalisa mai wakiltar mazabar Bida II, Haruna Baba ya tabbatar da labarin.

Ya ce makonni biyu da suka gabata, mamba mai wakiltar mazabar Gurara, Binta Mamman ta kamu da cutar, lamarin da ya tilasta wa dukkan ‘yan majalisar zuwa yin gwajin cutar.

“Sai dai abin takaici, kakakin majalisar da akawun ta sun kamu da ita,” inji shi.

Ya kuma ce dukkan ‘yan majalisar da sauran shugabanninta tuni su ka killace kan su.

Wata majiyar kuma da ba ta amince a ambaci sunanta ba a majalisar ta shaida wa ‘yan jarida cewa sakamakon gwajin yawancin ‘yan majalisar ya nuna ba sa dauke da cutar in banda na Shugabanta da na Akawu.

Aminiya ta gano cewa tuni gwamnatin jihar ta umarci ma’aikatanta su fara aiki daga gida daga ranar Litinin domin takaita yaduwar cutar yayin da aka rufe dukkan makarantun jihar tun ranar Juma’a.