✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar zartaswa ta amince a cika wa ’yan kwadago alkawura

Majalisar zartaswa ta amince a koma amfani da kankare wajen gina tituna a Najeriya

Majalisar Zartarwa ta Kasa ta wahalar wa Gwamnatin Tarayya ta cika alkawuran da ta yi wa ’yan kwadago da ya sa kungiyar NLC ta janye yajin aikin da suka shirya shiga.

Ministan Kwadago, Simon Bako Lalong ne ya sanar da haka bayan taron majalisar ministocin da Shugaba Tinubu ya jagoranta a ranar Litinin.

Majalisar zartarwar, wadda ta sauya ranar zamanta zuwa Laraba, ta kuma amince da komawa amfani da ƙanƙare wajen aikin gina tituna a maimakon kwalta, domin kara ingancin titunan Najeriya.

Ministan Ayyuka Umahi ya bayyana cewa, “za a ci gaba da amfani da kankare a ayyukan titunan da ake kan yi a halin yanzu.

“Sannan majalisar ta wahalar a fara aikin gyaran titin Legas-Fatakwal-Kalaba, da kuma titin da ya tashi daga Sakkwato zuwa Ogoja,” inji Umahi.

Ya ci gaba da cewa zaman yakuma amince hukumar tara haraji ta kasa (FIRS) da kamfanin NNPC su ci gaba da lura da kuma daukar nauyin ayyukan tituna da ke karkashin kulawarsu.

Sannan  duk jihar da ke son gyarar titin Gwamnatin Tarayya da ya ratsa ta cikinta, za ta samu sahalewa cikin awa 24, bisa sharadin sai ingancin aikin ya cika sharuddan da Gwamnatin Tarayya ta tsara da kuma tsarin shingen karbar kudin haraji a kan titunan, domin su maida da kudadensu.

“Za kuma a kammala duk abin da ya kamata a yarjejeniyar aikin tituna takwas da gwamnatin da ta gabata ta ba wa ’yan kasuwa zuwa watan Nuwamba.

Tinubu zai jagoranci kwamitin bunkasa masana’antu

Ministar Masana’antu da Zuba Jari, Doris Uzoka-Anite, ta ce majalisar ta amince da kafa kwamitin farfado da masana’antu da zuba jari a karkashin jagorancin Tinubu.

Kananan kwamitoci takwas da ke karkashin kwamitin shugaban kasar sun hada da na bayar da rance, musayar kaya, bunaksa tama, lasisin kananan masana’antu, mai da iskar gas, bangaren nishadi, ma’adiniai da sauransu.

Muna sa ran hakan zai bunaksa zuba jari, samar da ayyukan yi masu inganci, da kuma bunƙasa kayayyakin da ake samarwa acikin gida da kimanin Naira tiriliyan daya, in ji Uzoka-Anite.

Ta bayyana cewa kwamitin yankunan kasuwanci marar iyaka zai bullo da tsare-tsare domin samar da karin damarmaki ga ’yan Najeriya.

An kuma kafa kwamiti da zai kula da tsarin kasuwanci marar kaidai domin yin sabbin sauye-sauyen inganta shi, domin jama’ar kasa da sauran masu zuba jari su amfana.