✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Malamai da tsoffin sojoji ba sa kwazo a jagoranci —Obasanjo

Akasari ba a mulki mai kyau saboda rashin samun mataimaka na gari.

Tsohon Shugaban Kasa, Cif Olusegun Obasanjo, ya ce galibi ba a samun wani ci gaba na a zo a gani a jihohin da suka kasance karkashin jagorancin malamai ko tsofaffin soji.

Obasanjo ya ce babu wani ci gaban da aka samu a jihohin kasar nan da ke karkashin jagorancin mutane masu rike da matsayin Farfesa ko Dakta da tsoffin sojoji, har ma da malaman makarantu.

Tsohon Shugaban na Najeriya na wannan furuci a jawabinsa yayin wani taro kan zurfafa al’adun dimokuradiyya da aka gudanar ranar Alhamis a Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas.

Obasanjo ya ce duk da yake an samu wasu jajirtattun shugabannin da ba su da yawa, akasarinsu ba sa iya mulki mai kyau saboda rashin samun mataimaka na gari, abin da ke hana su jagorancin da ake bukata.

A cewarsa, rashin tattaunawa tsakanin shugabannin da masu taimaka musu, kan haifar da gibi wajen musayar ra’ayi, matakin da ke hana samun fahimtar juna da hadin-kai wajen cimma manufar ci gaba da ake bukata.

Obasanjo ya ce, bayan kwashe shekaru 60 da samun ‘yancin kan Najeriya, har yanzu shugabannin kasar sun kasa samar da yanayin shugabanci mai inganci wanda zai samar wa kasar ci gaba da kuma magance banbance-banbancen da ake samu na kabilanci da addini da kuma shiya.

Obasanjo ya ce, yadda ake tafiyar da dimokuradiyyar Najeriya ya haifar da rabe-raben kawuna da mummunar alaka da rashin amince wa juna da kuma rashin kishin kasa a tsakanin jama’a da kuma al’umma a sassan kasar.

Obasanjo ya ce, abin takaici ne yadda karya da zage-zage da son kai suka mamaye yakin neman zaben da ake gudanarwa yanzu haka, maimakon gabatar da shirin da ake da shi na gina kasa.

A halin yanzu dai jihohin Borno da Cross Rivers ne kawai ke da masu rike da mukamin Farfesa da ke jagorancin su a matsayin gwamnoni, yayin da ake da wasu masu mukamin Dakta.