✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manoma 4 sun mutu a hatsarin kwalekwale a Nasarawa

Hatsarin ya rutsa da manoman yayin da suke hanyar dawowa daga gonakinsu.

Akalla mutum hudu ne suka mutu a wani hatsarin kwalekwale a Karamar Hukumar Awe da ke jihar Nasarawa.

Aminiya ta gano cewa kwalekwalen da ke jigilar manoman shinkafa daga gundumar Ubbe a Karamar Hukumar Nasarawa Eggon, ya kife ne a wani kogi da ke kauyen Hunki na Karamar Hukumar Awe a ranar Litinin da daddare.

Wakilinmu ya samu labarin cewa tuni aka kwaso gawarwakin wadanda suka mutu zuwa kauyen domin tantance su.

Wadanda suka mutu sun hada da Alkali Congo, Shedrack Dauda, Mashack Dauda, da kuma Akolo Moses.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, DSP Ramhan Nansel, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a Lafiya, babban birnin Jihar a ranar Talata, ya bayyana cewa har yanzu ba a gano direban jirgin ba.

Ya ce, “Lamarin ya faru ne jiya [Litinin]; manoman na dawowa daga gona lokacin da kwalekwalen ya kife.

“Amma an gano gawarwaki hudu, kuma an ceto mutum daya daga cikinsu.

“Sai dai har yanzu ba a gano matukin jirgin ba, amma ana ci gaba da kokarin gano shi.

Mukaddashin Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar ya jajanta wa iyalan wadanda suka mutu, ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan su.”

Wakilinmu ya ruwaito cewa, a baya-bayan nan mutum 12 ne suka rasa rayukansu sakamakon wani hatsarin kwale-kwale da ya rutsa da su a kogin Kogi Kungra Kamfani da ke unguwar Arikiya a karamar hukumar Lafia.