✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu kai wa ’yan bindigar Kaduna burodi sun shiga hannu

Ya ce ya kan sami kusan N150,000 a kowanne mako ta hanyar kai musu burodin.

Daya daga cikin masu gasa burodin da aka cafke yana kai wa ’yan bindiga burodin ya bayyana ’yan bindigar da suka addabi mazauna Jihar Kaduna a matsayin manyan kwastomominsu.

Masu gasa burodin dai su uku da dubunsu ta cika bayan ’yan sanda sun cafke su a Kaduna sun amsa cewa sune suke kai wa ’yan ta’addan burodi.

’Yan bindigar dai na aika-aika ne a yankunan Damari da Kidandan da Awala da ke Kananan Hukumomin Birnin Gwari da Giwa a Jihar ta Kaduna.

Wadanda ake zargin dai sun yi wa ’yan sanda jagora har zuwa masana’antun da suke gasa burodin.

Daya daga cikin wadanda aka kama wanda dan asalin Galadimawa ne ya ce ya fara harkar gasa burodi ne tun a shekarar 2018.

Ya ce, “A da ni dan acaba ne wanda a baya a lokuta da dama ’yan bindiga kan kwace mana babura. Daga bisani sai wani dan uwana ya zo garinmu ya koya min gasa burodi, da ’yan kudaden da na tara sai na fara sana’ar.

“Na fara ne da N21,000, amma yanzu na kan sami N400,000 a kowanne wata. Hakan kuwa ta faru ne lokacin da na fara kai wa ’yan bindiga  burodin.

“A nan aka haifeni a Galadimawa kuma a nan na taso kuma na san matasanmu da dama da suka fada harkar bindigar.

“Muna da kyakkyawar alaka da su saboda ba sa kawo mana hari. Da farko da suka fara su kan mamaye kauyukanmu, amma da wasu shugabannin al’umma suka kira su suka nuna musu ba mune musabbabin matsalolinsu ba, sai suka daina,” inji shi.

‘Yadda na fara haduwa da ’yan bindiga’

Wanda ake zargin ya ci gaba da cewa ya fara haduwa da ’yan bindigar ne a shekarar 2019, lokacin da ya hadu da daya daga cikinsu wanda ya sayi sinki 10 na burodin, sannan ya dauki lambar wayarsa a jikin ledar burodin.

Ya ce, “A lokacin na sayar masa da kowanne sinki daya a kan N200, sabanin N170 da ake sayarwa.

“Kashe-gari sai ya kira ni ya ce burodin nawa akwai dadi, suna bukatar karin sinki 20.

“A wannan ranar na kai musu, inda na tarar da wasu mutum uku a wurin, wadanda suka ce suna so na rika kawo musu da yawa, amma sai nace musu bani da isasshen jari. A nan ne suka amince cewa za su rika bani kudin tun ma kafin na gaso burodin.”

‘Na kan iya samun ribar N150,000’

“Da farko na N20,000 suka fara saye, sai suka kara zuwa N50,000 a kullum. Bayan cire kudin kayayyakin hadi, na kan iya samun kamar N150,000 a kowanne mako.

“Muna da wurin da muke haduwa da su a kusa da wata maboyarsu, kasancewar basa barina na shiga cikin dajin, ko mota ma bata iya shiga. Ba sa yi min kowacce irin barazana saboda kowa kawai harkarsa yake yi.

“Ban san komai a kan harkarsu ta garkuwa da mutane ba, ni kawai burodi nake sayar musu in kama gabana.

“Daya daga cikin ma’aikatana ne ya fada hannun ’yan sanda a kan hanyarsa ta kai musu burodin, inda su kuma suka tiso keyarsa zuwa gidan burodin namu,” inji shi.