✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu Zanga-Zangar cire tallafin mai Sun Ɓalle Ƙofar Majalisa

Masu zanga-zangar sun balla kofar sun shiga majalisar da karfin tuwo ne bayan takaddama da jami'an tsaro

Masu zanga-zangar cire tallafin mai da ƙungiyoyar ƙwadago ta kasa (NLC) ke jagoranta sun ɓalle ƙofar shigar majalisar dokoki ta ƙasa.

Rahotanni sun nuna fusatattun masu zanga-zangar ta NLC da takwararta TUC sun balla kofar tare da shiga su mamaye majalisar ne bayan takaddama da jami’an tsaro da ke gadin harabar majalisar.

Sun isa wurin ne bisa jagorancin shugaban NLC Joe Ajaero da takwaransa na TUC Festus Osifo, inda suka bukaci jami’an tsaron sun bude musu domin su shiga su gabatar da korafinsu, amma jami’an tsaro suka ki.

Ana cikin haka ne ’yan kungiyar suka yi kukan kura suka karya kokar suka kutsa cikin harabar majalisar da karfin tuwo domin huce haushinsu, bayan sun faro tattakin tun daga Unity Fountain zuwa Majalisar.

Bayan nan ne Sanata Ali Ndume daga Jihar Borno da kuma Ireti Kingibe daga suka gana da masu zanga-zangar, wadanda suka bakaci:

  1. Soke daukacin dokoki da tsare-tsaren Gwamnatin Tinubu da suka jefa mutane cikin wahala.
  2. Gyara matatun mai domin daina shigo da shi daga kasashen waje
  3. Aiwatar da tsarin amfani da iskar gas (CNG) ya maye gurbin fetur
  4. Rage kudin da ake kashewa wajen gudanar da gwamnati – TUC
  5. Biyan albashin wata takwas na malaman jami’a da suka yi yakin aiki a 2022.
  6. Majalisa ta nuna kishi da sadaukarwa a yanayin ayyukanta.
  7. Ci gaba da tattaunawar NLC da gwamnati kan sabon mafi karancin albashi.

Da yake jawabi shugaban NLC, Joe Ajaero, ya ce sabanin ikirain Shugaba Tinubu na rage kashe Naira tiriliyan daya bayan janye tallafin mai, kwamitin da gwamnati da ke tattaunawa da su, ya shaida musu cewa ko sisi ba a samu ba.

Cire tallafin mai da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi tun a jawabinsa na bayan karbar rantsuwar fara aiki ya sa farashin fetur tahin gwauron zabo daga N197 zuwa 620.

Hakan ya haifar ta hauhawar farashin kayan masarufi da na sufuri, wanda kawo yanzu ’yan kasar ba su ga alamar sassautawarsu

Hakazalika, duk da karin farashin da aka samu na wadandannan kayayyakin bukatu na yau da kullum, har yanzu ba a yi musu karin albashi ba.

Ko da yake gwamnatin kasar ta sanar da shirinta na ba da tallafin N8,000 a duk wata na tsawon wata 6 ga masu tsananin bukata guda miliyan 12 a kasar, matakin da al’ummar kasar ke ganin mara amfani ne.