✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mata 500 sun amfana da tallafin gwamnatin tarayya a Kwara

Kimanin mata 500 ne a Jihar Kwara suka amfana da tallafin tsabar kudi daga Gwamnatin Tarayya a ranar Litinin.

Kimanin mata 500 ne a Jihar Kwara suka amfana da tallafin tsabar kudi daga Gwamnatin Tarayya a ranar Litinin.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya rawaito cewa an raba tsabar kudin N20,000 ga matan mazauna karkara a dakin taro na Convolis dake Sango a Ilorin, babban birnin jihar.

Rahotanni sun ce Ministan Watsa Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya jagoranci raba kudaden ga matan da suka amfana.

Jagoran shirin daga Ma’aikatar Jin-kai ta kasa, Dokta Abubakar Suleiman, ya ce shirin an bijiro da shi ne don tallafawa matan karkara don su inganta rayuwarsu da ta iyalansu.

“Manufar bayar da tallafin shi ne su bunkasa sana’o’insu ta yadda za su kyautata rayuwarsu ta hanyar abunda suke samu, wanda sannu hankali za su cimma muradinsu,” In ji shi.

Wasu daga cikin matan da suka amfana da shirin sun bayyana farin cikinsu kan shirin na jin-kai daga Gwamnatin Tarayya, sun kuma ce bayar da tallafin ya zo a daidai lokacin da suke bukatarsa.

Misis Comfort Olanrewaju daga karamar hukuma Ilorin ta Kudu, ta ce ta yi farin ciki da ta samu kanta cikin wadanda suka amfana da tallafin kudin.

“Na yi matukar farin ciki saboda tallafin kudin ya zo lokacin da nake bukata. Na ji dadi matuka saboda kasuwanci na ba ya tafiya yadda ya kamata a daidai wannan lokacin,” In ji ta.