✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matan aure sun kashe kasurgumin dan ta’adda a Taraba

Gunduwa-gunduwa aka yi wa sassan jikin dan ta’addan.

Fusatattun mata da hare-haren ’yan bindiga suka raba da mazajensu sun kashe wani kasurgumin dan ta’adda mai suna Maliya a Jihar Taraba.

Aminiya ta ruwaito cewa ’yan banga ne suka kama dan ta’addan wanda aka dade ana nema ruwa a jallo.

’Yan banga sun sami nasarar kama dan ta’addan ne a garin Kunguna da ke Karamar Hukumar Karim Lamido.

Maliya ana zarginsa da sace mutane masu yawan gaske tare da hare-haren ta’addanci a wurare daban daban a yankin Karamar Hukumar Karim Lamido da wasu sassa na jihohin Filato da Bauchi.

Bayanai sun nuna cewa daga bisani ne dan ta’addan ya tsere zuwa yankin Karamar Hukumar Bali ya hadu da wasu gungun ’yan ta’addan.

’Yan banga sun kai dan ta’addan gari Binnari inda ake zargin ya kashe mutune masu yawan tare da garkuwa da mutane da dama.

Wani mazaunin garin Mayoreniyo da ke Karamar Hukumar Ardo Kola mai suna Abubakar Sani ya shaida wa wakilin Aminiya cewa, “a lokacin da ’yan bangar suka shiga garin Binnari da dan ta’addan sai jama’ar gari maza da mata suka nemi a ba su shi su kashe shi.

Ya kara da cewa, “mata wadanda dan ta’addan ya kashe mazajensu ne suka kwace dan ta’addan daga hannun ’yan banga suka kashe shi.

“Gunduwa-gunduwa aka yi wa sassan jikin dan ta’addan,” a cewar Abubakar Sani.

Kokarin jin na bakin kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Taraba DSP Usman Abdullahi kan wannan lamari ya ci tura domin wayoyinsa a rufe suke a lokacin da wakilin Aminiya ya nemi jin karin bayani daga wurinsa.