✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matar attajiri Aminu Dantata ta rasu

Ta rasu ne a wani asibiti da ke Jiddah, kasar Saudiyya

Daya daga cikin matan attajirin nan na Jihar Kano, Alhaji Aminu Dantata, Hajiya Rabi Dantata, ta rasu.

Marigayiyar wacce aka fi sani da Mama Rabi dai ita ce mahaifiyar fitaccen dan kasuwar nan, Tajuddeen Dantata.

Majiyoyi daga iyalan marigayiyar sun ce ta rasu ne ranar Asabar a wani asibiti da ke birnin Jiddah na kasar Saudiyya.

Ta rasu tana da shekara 70, bayan fama da gajeruwar jinya.

Daga cikin ’ya’yan da ta bari akwai Tajjuddeen Dantata da Batulu Dantata da Hafsa Dantata da Jamila Dantata da kuma Aliya Dantata, da kuma jikoki masu yawa.