✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashi ya datse wa tsohuwa kai a Kalaba

Wata majiya ta ce bayan ya make ta, ta fadi sumammiya, sai ya bi ta da adda ya sare ta.

Wani matashi mai suna Christian Eden Eyo da ke Unguwar Mnakpa yankin Karamar Hukumar Kalaba ta Kudu ya yi wa wata makabciyarsa kwanton bauna ya bige ta da makami bayan ta fadi kasa ya sanya adda ya datse mata kai.

Matar mai suna Misis Uduak ta yi asubanci za ta tafi ta yi wanka ashe Eden Eyo na labe a kan hanyar da makaminsa.

Matar na zuwa za ta wuce ba ta sani ba, ya maka mata makami ta fadi warwas.

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa, bayan ya make ta, ta fadi sumammiya, sai ya bi ta da adda ya sare ta.

Makwabtansu da suke gida daya da Ekamma Anniefiom da Anestha Eyo sun shaida wa wakilinmu cewa, “Muna dawowa daga Coci ne sai muka ga alamun jini faca-faca a gidan, da muka bi sawu, sai muka ga ya nufi dakin Christian. Nan take muka ga yana kokarin binne gawar bayan mun labe muna kallon abin da yake yi, bai sani ba.”

Wakilinmu ya tuntubi makwabcin silar rikicin, sai ya ce ko dama can ba a ga maciji tsakaninsu “Wata rana ce akaji su suna cacar baki kuma kowannensu zaman kansa yake yi, zaman gidan haya ne ya hada su.”

Aminiya ta tuntubi mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Kuros Riba, Irene Igbo inda ta tabbatar da faruwar hakan.

Ta ce “Wanda ake zargin na hannu ana yi masa bincike, da zarar an kammala za a mika shi ga kotu.”