✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matashi ya kashe kansa bayan ya soki mahaifinsa da wuka a Zariya

Mahaifin nasa dai tsohon lakcara ne a ABU Zariya

Wani matashi ya kashe kansa ta hanyar fadowa daga gadar sama ta Dan-Magaji da ke Zariya, bayan ya sossoki mahaifinsa, wanda tsohon lakcara ne a Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), da wuka.

Marigayi Akudi Gideon mai kimanin shekara 40 dai ya kashe kan nasa ne bayan ya sossoki mahaifin nasa, Gideon Tseja (TAMAZA), mai shekaru 75 da wuka.

Matashin, mazaunin unguwar Wusasa ne da ke karamar hukumar Zariya a Jihar Kaduna, kuma lamarin ya faru ne da safiyar Asabar, 25 ga watan Satumban 2022.

Majiyar Aminiya ta ce sanannen matashi ne wajan yin ta’ammali da kayan maye kuma wadda bai cika shiga cikin mutane ba sosai.

Majiyar ta kara da cewa yana zaune ne a gida daya da mahaifin nasa wanda ya riga ya stufa tukuf.

Majiyar ta kara da cewa bayan fadowar Akudi ne daga kan gadar, sai aka je gidansu domin a sanar da iyalansu, inda aka sami mahaifin cikin jini.

Daga bisani ne aka gane cewar a shi ne ya sossoki mahaifinsa da wuka kafin ya je ya hau kan gadar saman ya fado, inda kanshi ya fashe kuma nan take ya mutu.

Da yake yi wa wakilinmu karin bayani, Dagacin Wusasa, Injiniya Isyaku Yusuf, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce, “Shi Gideon Tseja (TAMAZA) tsohon malamin ne a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, kuma marubuci ne sosai, sai dai shekaru ya ruskeshi.”

Inda yanzu haka mahaifin Mista Gideon, yake kwance a Asibiti Wusasa yana samun kulawar likitoci.