✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashin da ya hallaka abokinsa a Kano ya shiga hannu

Ya kasho abokinsa bayan sun samu sa-in-sa a tsakaninsu

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta cafke wani matashi mai kimanin shekaru 18 bisa zargin sa da kashe abokinsa.

Kakakin rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da mutuwar matashin mai Suna Ibrahim Khalil da ke unguwar Kofar Mazugal a Karamar Hukumar Dala ta jihar.

Kiyawa yace, lamarin ya faru ne sakamakon sa-in-sa da aka samu tsakanin marigayin da wani mai kimanin shekaru 18.

Wanda ake zargin ne ya hasala, har ta kai ga ya hau dukan Ibrahim har lahira.

Bayan an kai  shi asibitin Murtala da ke Kano, likitoci suka tabbatar da ya rasu.

Tuni dai rundunar  ta samu nasarar damke matashi da ake zargin, domin gurfanar da shi a gaban kuliya.