✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rasha ta sace Daraktan Masana’antar nukiliyar Ukraine

Sojojin Rasha sun yi gakuwa da Mataimakin Darakta-Janar na Sashen Kula da Ma'aikta a Masana'antar Nukiliya ta Zaporizhzhia, Valeriy Martyniuk

Sojojin Rasha da sun yi awon gaba da wani Dakarta-Janar da ke aiki a masana’antar nukiliyarta ta Zaporizhzhia.

Gwamnatin Ukraine na zargin dakarun Rasha da azabtarwa da kuma wulakanta babban jam’in a masana’natar nukiliyar da ke yakin Kudancin Ukraine da ke karkashin ikon sojojin Rasha.

“Sojojin Rasha sun yi gakuwa da Mataimakin Darakta-Janar na Sashen Kula da Ma’aikta a Masana’antar Nukiliya ta Zaporizhzhia, Valeriy Martyniuk,” in ji sanarwar da gwamnatin Ukraine ta fitar a ranar Talata.

Sanarwar ta yi kira ga Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) Rafael Grossi da zai kai ziyara Rasha da ya sa baki Rasha ta sako jami’in.