✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matawalle zai gina kwatocin miliyan 692 a Gusau

Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayar da kwangilar Naira miliyan 692 domin gina kwatoci da kwalbatoci a Gusau babban birnin Jihar. Kwamishinan Ayyuka da Sufuri Ibarihm…

Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayar da kwangilar Naira miliyan 692 domin gina kwatoci da kwalbatoci a Gusau babban birnin Jihar.

Kwamishinan Ayyuka da Sufuri Ibarihm Isah Mayana ya ce za a fara aikin ne a karshen watan Nuwamba bayan janyewar damina domin rage barnar da ambaliya ke yi a garin na Gusau.

“Fadi da zurfin kwatocin ya kai mita 1.5 zuwa mita 3 har zuwa mita 6, tsayin kuma zai kai mita 2200. Sannan za a gina kwalbatoci a wurare daban-daban.

“Kwatocin za su fara daga ’Yar Dorayi – Gadar Abu Magaji – Gusau Hotel har zuwa kududdufin da ke bayan masakar Zamfara Textile.

“Hakan zai taimana wajen kawar da ambaliyar da ake samu kowace shekara a birnin”.

Ya ci gaba da cewa aikin “na daga cikin alkawuranmu na neman zabe cewa za a gina magudanan ruwa da tituna a sassan jihar”.

Kwamishinan ya ce Gwamna Bello Matawalle zai kuma gina tituna a cikin garin Gusau a kokarinsa na kara kawata garin.

Ibrahim wanda ya bayyana bukatar yi wa magudanan ruwa gyaran fuska, ya yi kira ga jama’ar jihar da su kula da ayyukan ta hanyar daina zubar da shara barkatai.