✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matsalar tsaro: Matasa sun yi zanga-zangar lumana a ’Yantumaki

Sun yi kira ga gwamnati da ta dauki matakin kare lafiya da dukiyoyinsu.

Da safiyar ranar Litinin ne wasu fusatattun matasa suka rufe babban titin Katsina zuwa Kankara a garin ’Yantumaki don nuna bacin ransu kan yadda sha’anin tsaro yake kara tabarbarewa a yankin.

Matasan, wadanda suka rika kone tayoyi tare da tare motoci sun yi kira ga gwamnati da ta dauki mataki don kare lafiya da dukiyoyin jama’ar kauyukan da suke kewaye da garin, wanda suka ce ’yan bindiga sun addabe su da kisa da kuma satar dabbobi.

Da yake wa Aminiya karin bayani, wani matashi mai suna Danladi, ya bayyana cewa lamarin rashin tsaro na kara kamari a yankin, inda a kullum sai maharan sun shiga kauyukansu sun kashe mutane tare da sace masu dabbobi.

“Ko a daren jiya sai da suka share fiye da sa’o’i uku a kauyen Amarawa inda suka kashe mutane biyu da jikkata da dama tare da kore kaf dabbobin garin.

“Daga bisani sun shiga garin Dan-Ali. Abin takaicin kuma shi ne babu wasu jami’an tsaro da suke kawo mana dauki,” Inji shi.

Ya ci gaba da cewa “A halin yanzu garin ’Yantumaki cike yake makil da ’yan gudun hijira wadanda suka baro kauyukansu, musamman daga gabacin garin.”

Haka kuma ya tabbatar wa Aminiya cewa akwai jami’an soja a garin amma basa kai dauki ga jama’a duk kuwa da cewa ana kokarin sanar da su a yayin da maharan ke cin karensu ba babbaka a kauyukan.

“Akwai sojoji da aka kawo nan, amma ba sa kai wa jama’a dauki ko da an sanar da su. Ga su nan ma yanzu suna ihu bayan hari suna ta yin harbi sama a banza wa matasa masu zanga-zanga.”

Ko a baya, garin na ’Yantumaki da ke Karamar Hukumar Danmusa ta Jihar Katsina ya sha fama da hare-haren ’yan bindiga wadanda suka yi sanadiyyar rasuwar Hakimin garin a daya daga cikin hare-haren.

Karamar Hukumar Danmusa tana daya daga cikin yankunan da suke fama da mummunar matsalar tsaro inda mahara ke cin karensu ba babbaka a cikinta.