✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matsalar tsaro: Sanatoci sun yi barazanar tsige Buhari

Sun ba Buharin mako shida ya magance matsalar ko su tsige shi

Sanatocin jam’iyyun adawa sun ba Shugaban Kasa Muhammadu Buhari wa’adin mako shida ya kawo karshen matsalar tsaron da ta addabi Najeriya ko su tsige shi.

Shugaban Marasa Rinjaye na majalisar, Philip Aduda, shi ne ya bayyana hakan lokacin da yake jawabi ga manema labarai bayan ’yan majalisar na jam’iyyun adawar sun mamaye zauren majalisar cikin bacin rai a ranar Laraba.

’Yan majalisar dai sun rika rera wakokin “Dole Buhari ya sauka, dole [Ahmed] Lawan ma ya bi sahun shi,” don nuna bacin ransu a kan matsalar tsaro a Najeriya.

Hatsaniya dai ta barke a majalisar ne a lokacin da Shugaban Marasa Rinjayen ya taso da batun matsalar tsaron, bayan an shafe awa biyu ana tattauna shi cikin sirri.

Shugaban Majalisar, Sanata Ahmed Lawan bayan kammala zaman ya sanar da cewa sun tattauna batutuwa masu alaka da ayyukan majalisar da kuma hadin kan Najeriya, sannan ya umarci shugabannin majalisar su ci gaba da aiki kan abubuwan da aka tattauna a kai.

To sai dai Sanata Philip Aduda ya taso da batun tattauna abubuwan da suka yi a zaman na sirri, amma Lawan ya hana shi magana.

Hakan dai ya jawo ran ’yan majalisar na bangaren adawa ya baci, inda suka mamaye zauren majalisar, suna rera wakokin neman Buharin ya sauka.