✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsananciyar yunwa za ta kashe kananan yara 300,000 a Somaliya —MDD

Daya cikin kowane mutum hudu a Somaliya na fama da matsananciyar yunwa

Majalisar Dinkin Duniya ta ce matsananciyar yunwa na barazanar kisa ga kananan yara 300,000 ’yan kasa da shekara biyar a kasar Somaliya a cikin ’yan watanni masu zuwa.

Majalisar ta bayyana cewa a halin yanzu mutum daya cikin kowane mutum hudu na fama da matsananciyar yunwa sakamakon rashin ruwan sama a Somaliya, inda akalla mutum miliyan 4.6 ke iya fadawa cikin matsanciyar bukatar abinci daga yanzu zuwa watan Mayun 2022.

Kodinetinta na Ayyukan Jin Kai A Somaliya, Adam Abdelmoula, ya ce kananan yara 300,000 ’yan kasa da shekara biyar da ke fuskantar hadarin matsananciyar yunwar, “Za su iya mutuwa idan ba su samu dauki da wuri ba.”

Minisatar Agaji da Ayyukan Jin Kai ta Somaliya, Khadija Diriye, ta ce, “Babbar matsalar ita ce idan muka rasa agajin gaggawa, yunwa za ta fara kashe mata da kananan yara da maza.”

A halin yanzu dai Majalisar Dinkin Duniya na neman tallafin kayan agaji na Dala biliyan 1.5 domin shawo kan matsalar a Somaliya, wadda a watan Nuwamba gwamantin kasar ta ayyana rashin ruwan sama a matsayin ibtila’i.

A yayin da damina ke kara karatowa, zanzu shekara uku ke nan a jere da ake fama da karancin ruwan sama a kasar ta Somaliya, wanda rabon da hakan ta faru an fi shekara 30.

Tuni karancin abinci da ruwan sha da wurin kiwo ya tilasta wa mutum sama da 169,000 kaura daga garuruwansu a kasar.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi hasashen yawan mutanen da ke kaura daga kasar a sakamakon haka zai karu zuwa miliyan 1.4 a cikin wata shida masu zuwa.

Sanarwar da ta fitar ta ce ibtila’o’i su ne manyan dalilan da ke sa mutane yin kaura —ba yaki ba — a  kasar da ta jima tana fama da yaki kuma take cikin manyan wadanda saunyin yanayi ya fi yi wa illa.

Ta ce zuwa 2022 matsalar za ta kara tsananta da kashi 30 cikin 100 ta yadda kusan rabin ’yan kasar za su bukaci agaji da kuma kariya.

A halin yanzu mutum bakwai cikin kowane mutum 10 a kasar matalauta ne, gami da karancin ruwan saman da ya kara wa lamarin tsanani.

Iyalai na asarar dabbobinsu da ke ta mutuwa, ga kuma hauhawar farashin kayan masarufi sakamakon karancin amfanin gona.

Tun a 2017 yankin Gabashin Afirka ya fara fama da karancin ruwan sama, lamarin da ya haifar da karancin abinci a Somaliya, gami da barkewar cututtuka masu alaka da rashin tsaftataccen ruwan sha.

Masana sun alakanta matsalar da sauyin yanayi.