✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Minista na so a haramta sayar da giya a tashoshin mota a Najeriya

Minista a Ma’aikatar Sufuri, Ademola Adegoroye, ya ce sayar da giya a tashoshin mota ko duk inda direbobi ke hutawa ba abin ne da ya…

Minista a Ma’aikatar Sufuri, Ademola Adegoroye, ya ce sayar da giya a tashoshin mota ko duk inda direbobi ke hutawa ba abin ne da ya dace ba.

Ministan ya yi wannan kiran ne yayin da shugabannin Kungiyar Direbobi ta Kasa (NURTW), suka kai masa ziyara Abuja.

Ya kuma ce akwai bukatar samar da dokoki da tsari ga sana’ar domin daidaita ta a Najeriya, kamar yadda sauran kasashen duniya suke yi.

Shugaban Kungiyar Direbobi ta Kasa (NURTW), Tajudeen Ibikunle Baruwa, ya bayyana hakan ne lokacin da ya jagoranci wasu jami’an kungiyar na kasa ziyarar ban girma ga ministan domin amincewa da shirin da ma’aikatar sufuri ta tarayya ta yi na samar da sabon shirin sufuri da zai samar da sabbin motoci ga direbobin kasar.

A kwanakin baya ne dai ma’aikatar sufuri ta kasa ta kafa kwamitin aiwatar da shirin na musamman kan zirga-zirgar ababen hawa da su kansu direbobin, domin saukaka sufurin ababan hawa a fadin kasar nan.

Ya kuma ce kungiyar za ta magance matsalar tukin ganganci ta hanyar horar da mambobinsu illar shan miyagun kwayoyi yayin aiki.

Shugaban kungiyar ya ce direbobi a fadin kasar nan, na farin ciki da shirin, kuma za su hada hannu da Gwamnatin Tarayya domin tabbatar da an aiwatar da shi cikin nasara.