✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ministan Cikin Gidan Ukraine da wasu mutum 14 sun mutu a hatsarin jirgin sama

Sai dai babu cikakkun bayanai kan musabbabin hatsarin

Akalla mutum 15, ciki har da Ministan Harkokin Cikin Gidan Ukraine, Denys Monastyrskyy da wasu yara uku sun mutu a wani hatsarin jirgin sama ranar Laraba a dab da Kyiv, babban birnin kasar.

Jirgin, mai saukar angulu dai ya kashe Ministan ne da Mataimakinsa, Yevhen Yenin, da kuma Sakataren Ma’aikatar, Yurii Lubkovych, kamar yadda Shugaban ’Yan Sandan Kasar, Ihor Klymenko ya sanar.

To sai dai babu cikakken bayani kan musabbabin hatsarin da ya faru a garin Brovary, daya daga cikin garuruwan da Rasha ta kaddamar da hare-harenta kan Ukraine a bara.

Rahotanni sun ce mutum 29 sun jikkata, ciki har da yara 15 da ke wata makarantar Nazire da wasu malamansu da ke aiki tare.

Wasu hotunan bidiyo da aka wallafa a kafafen sada zumunta sun nuna wani gini na ci da wuta da kuma mutane na ihun neman taimako.

Wasu da dama kuma sun makale a gefen ginin makarantar da ya lalace, yayin da baraguzan ginin suka warwatsu a filin wasan makarantar.

Shugaban ’Yan Sandan ya ce tara daga cikin mutanen da aka tabbatar da rasuwar tasu a kan jirgin suke.

Ya kuma ce jirgin mallakin Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasar ce.