✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Motar haya ta kama wuta da mutum 18 a cikinta

Fasinjojin sun yi ta kansu tun kafin wutar ta kama ganga-ganga.

Wata motar haya dauke da fasinjoji 18 ta kama da wuta a yayin da take tsaka da tafiya da su.

Lamarin da ya faru ne a kauyen Komo Araromi da ke kan titin Ajase Ipo a Jihar Kwara, amma an auna arziki fasinjojin sun tsallake rijiya da baya.

Motar bas din da hakan ya ritsa da ita kirar Hiace ce, kuma ta taso ne daga Oshogbo a Jihar Osun, kwatsam sai ta kama wuta da misalin karfe 10:57 na safiyar ranar Alhamis.

Sai dai an yi sa’a daukacin fasinjojin motar sun fice daga cikinta a kan lokaci, babu wanda ransa ya salwanta.

Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) a Jihar Kwara, Jonathan Owoade, ya tabbatar wa Aminiya da faruwar lamarin ta wayar tarho.

Owoade ya ce wutar ta kama ne sakamakon yoyin man fetur a motar, wanda ya sa ta kama da wuta.