✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mu muka kwato yankuwan da Boko Haram ta kwace —Olanisakin

Ya ce ya bunkasa kwarewar sojoji, jin dadinsu da kuma samar musu da kayan aiki.

Tsohon Babban Hafsan Najeriya, Janar Abayomi Gabriel Olanisakin mai ritaya ya ce a karkashin shugabancinsa ne Rundunar Sojin Najeriya ta kwato daukacin garuruwan da a baya kungiyar Boko Haram ta mamaye.

Olanisakin ya ce a karkashin jagorancinsa Hedikwatar tsaro ta samu nasarori a bangaren bunkasa kwarewar sojoji, kula da jin dadinsu da kuma samar da kayan aiki.

Wadannan sun hada da kera kayan bukatun sojoji da suka hada da kananan jiragen ruwa, dafaffen abincin gwangwani, na’urar gano bom mai dogon zango da kuma na’urar sadarwa da ta kera da hakin gwiwar kamfanin Satcom.

A bangaren tsare-tsare da gudanarwa kuma, ya ce ya inganta tare da daga darajar wasu bangarori Hedikwatan Tsaron ta yadda za su fi yin tasiri.

Daga ciki akwai Sashen Hulda Tsakanin Sojoji da Fararen Hula wanda aka daga darajarsa domin bunkasa harkokin da ba na soji ba.

Ya bayyana hakan ne a lokacin bikin faretin bankwanan alfarma da aka shirya masa, bayan ya mika shugaban Hedikwatar Tsaro ga sabon Babban Hafsan Sojin Najeriya Manjo-Janar Lucky Irabor.

“A lokacin da Shugaba Buhari ya hau mulki Boko Haram na rike da 20 daga cikin Kananan Hukumomi 26 na Jihar Borno.

“Da muka fara aiki, babban abin da ke gabanmu shi ne kare Najeriya da kuma kwato yankunan daga hannun kungiyar.

“Goyon bayan da shugabannin siyasa da ’yan Najeriya suka ba mu ya taimaka wa sojoji a karkashin shugabancina suka kwato dukkannin yankunan daga hannun Boko Haram,” inji Janar Olanisakin mai ritaya.

Ya ce duk da matsalar ta’addancin da ke ci gaba da addabar Najeriya, sojoji za su ci gaba da taimaka wa gwamnati wajen yakar sauran kalubalen tsaro kamar yadda doka ta dora musu nauyin yin hakan.

Olanisakin ya yaba da zabin Manjo-Janar Lucky Irabor a matsayin sabbon Tsohon Babban Hafsan Sojin Najeriya.

Irabor tsohon Kwamandan Rundunar Operation Lafiya Dole ne kuma tsohon Kwamandan Rundunar Hadin Gwiwar Kasashe Masu Makwabtaka da Tabkin Chadi ne.

Uwa uba, kafin sabon mukamin nasa, Manjo-Janar Irabor shi ne Daraktan Sashen Horaswa da Tsare-tsare a Hedikwatar Tsaro.

“Babu wanda za a zaba da ya fi shi a matsayinsa na kwararren babban hafsan soji wanda nan ba da dadewa ba zai shiga aiki gadangadan,” inji shi.