✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Muhimman abubuwan da suka faru a Kannywood a 2021

A yau ne ake rufe wannan shekarar ta 2021, kuma kamar sauran shekarun da suka gabata, abubuwa da dama sun wakana a duniya, ciki har…

A yau ne ake rufe wannan shekarar ta 2021, kuma kamar sauran shekarun da suka gabata, abubuwa da dama sun wakana a duniya, ciki har da masana’antun fina-finai na duniya, musamman ma masana’antar fim ta Kannywood.

Aminiya ta yi tariya domin rairayo wasu muhimman abubuwan da suka faru a masana’antar da suka fi daukar hankalin mutane a wannan shekarar da take nade tabarma a yau.

Sauya akalar kasuwancin fina-finai

Abin da ya dade yana ci wa furodusoshi tuwo a kwarya a masana’antar Kannywood shi ne tabarbarewar kasuwancin fina-finan masana’antar da ya sa dole da yawa daga cikinsu suka koma gefe suna jiran yadda Allah zai yi da su.

Ana cikin haka ne wasu masu shirya fina-finan suka fara komawa kafar YouTube da nuna fina-finansu, wasu suka kuma talabajin, ga kuma sinima da ake dan gwadawa.

Haka kuma jarumai da mawaka sukan yi gamayya su shirya wakokin siyasa, inda nan ma suke samun kudaden shiga.

Wadannan abubuwan sun taimaka wajen fara dawo da martabar masana’antar, inda jarumai da mawaka da dama da aka daina jin duriyarsu suka dawo da karfinsu.

Binciken Aminiya ya gano cewa ba kamar yadda aka saba a baya ba, yanzu jaruman sun cire bambancin siyasa, inda suke neman arziki a tare.

Misali mawaka da dama sukan yi wa ’yan siyasa da daban-daban waka, ko su fito a wakar wannan, sannan su fito a wakar wani daban shi ma.

Haka kuma a fim din ‘Ka Yi Na Yi’ na Abubakar Bashir Maishadda, an samu kudi sama da Naira miliyan 5 a sinima daya kacal, wanda shi ma ba karamar nasara ba ce.

Mace-mace

Wani abin jimami kuma shi ne a daidai a lokacin da masana’antar ke ta kokarin farfadowa, sai ta rasa wasu daga cikin manyan jarumanta, wanda hakan ya jefa masana’antar da jarumanta cikin jimami.

Daga cikin wadanda suka rasu da aka fi yin jimami akwai Zainab Booth, mahaifyar Maryam Booth da Isiyaku Forest da Sani Garba SK da Ahmad Aliyu Tage da Alhaji Barau Yusuf da sauransu.

Rikicin Adam A. Zango da Ummi Rahab

Wani lamari da ya matukar tayar da kura a Kannywood a bana shi ne rikicin da ya barke a tsakanin Adam A. Zango da jaruma Ummi Rahab.

An fara sanin jarumar ce a fim din ‘Ummi’ na Abdul Amart Maikwashewa, inda suka fito tare da Adam A. Zango a matsayin ’yarsa da Jamila Nagudu a matsayin mahaifiyarta.

An fara samun matsalar ce bayan Adam A. Zango ya cire ta a fim dinsa mai suna Farin Wata, inda mutane suka fara tambayar dalilin yin hakan.

A wata tattaunawarsa da BBC Hausa a lokacin, Zango ya ce, “Kowa ya san ni da Ummi, sannan kuma duk mutumin da aka ce ka dauke shi a matsayin da ko ’ya, to sai dai ka yi ta yi masa addu’a a kan hanyar da ya sauya ya kuma bi idan marar kyau ce,” inji shi.

Adam Zango ya bayyana cewa tun Ummi tana da shekara 11 yake kula da ita, amma ba wai a hannunsa take ba, tana gaban iyayenta ne.

Ya ce sun yi hannun-riga ne saboda kauce wa umarnin da ya ba ta na ta rika gudanar da harkokin rayuwarta a bisa hanya madaidaiciya da ya dora ta a kai.

A cewarsa a lokacin: “Idan dai zan rike yaro in ce masa kada ya yi abu amma ya ce sai ya yi, to an yi kafin ita, kuma da aka zo kanta ma na ce to ta je Allah Ya bayar da sa’a.

“Na yi iya yina kuma na tabbatar da lokaci zai nuna cewa yadda take a lokacin tana wurina, da kuma yadda ta koma lokacin da ba ta wurina.”

Sai dai ana cikin haka ne yayan Ummin ya fito a bidiyo ya bayyana cewa Adam A. Zango ya nemi aurenta ne, ta nuna rashin amincewarta.

Da take nata jawabin, a wata tattaunawa da ta yi da Aminiya a wancan lokacin, Ummi ta ce, “Da farko ban yi niyyar magana a kan lamarin ba, saboda dan sabani ne na cikin gida aka yi ta terere da yamadidi da shi.

“Da yake Allah Ma jikan bawanSa ne sai ga wadansu mutane can daban da ko saninsu ban yi ba suka zo suna ta kare ni; Kai har sai da manyan mutane daga ciki da wajen masana’antar fim suka saka baki a ciki.

“Adam Zango yana kishi ne saboda na fara soyayya da wadansu samari, ya yi kokarin ya hana ni, amma na nuna masa cewa shi fa uba ne. Da ya ga ba zan yarda da ra’ayinsa ba shi ne ya fara bore.”

Game da cewa da ya yi shawara yake ba ta kan ta gyara, sai ta ce, “Sam ba haka ba ne, gaskiyar lamarin shi ne ya ce in aure shi ni kuma na ki yarda, kada ka dada kada ka kara.

“Na yi kokarin ya fahimce ni amma ya ki. Kuma ai al’umma sun san dabi’arsa ta son auren ’yan mata da yake aiki da su. Ni kuma gaskiya ba haka nake ba. Tun fa ina ’yar mitsitsiya nake tare da shi. To yaya zan auri wanda yake a matsayin babana?

“A kan maganar kunnen kashi kuwa ai kowa ya san Zango bai shahara da yayata sha’anin kula da addini da al’ada ba, kai akwai lokacin da ya sa ni na sanya wata sutura da ta jawo min bakin jini sosai, masoyana suka yi ta caccaka ta cewa kayan ba su dace ba. Har sai da iyayena suka ce idan na kara sanya irinsu za su hana ni yin fim kwata-kwata.

“To yanzu ka fada min wanda ya yi wannan shi ne za a ba wa amanar tarbiyya da har zai ce wani ba ya da kamun kai? Amma dai Allah Ya raya mu gaskiya za ta bayyana.”

Rashin lafiyar Maryam Yahaya

A watan Agusta ne aka fara rade-radin cewa jaruma Maryam Yahaya na fama da matsananciyar rashin lafiya, batun da ya tayar da kura, musamman a intanet.

An yi ta rade-radin cewa asiri aka yi wa jarumar, wadansu suna cewa cuta ce da ba a sani ba, inda wannan batu ya sa wadansu suke tambayar cewa wace irin cuta ce da ba a sani, kuma hakan ya sa wadansu suka kara tabbatar da batun cewa lallai asirin aka yi mata.

A lokacin jarumar ta fito ta bayyana cewa cutar maleriya ce da typhoid ta sha fama da ita.

Yanzu haka dai jarumar ta fara samun sauki, domin a farkon makon nan ta kai ziyara ofishin furodusa Abubakar Bashir Maisahadda.

Aure

A wani lamarin da ya jefa masana’antar cikin farin ciki kuwa shi ne wasu daga cikin jarumnta ne suka shiga daga ciki a 2021.

Daga cikin wadanda suka yi auren akwai jaruma Diamon Zahra da ta fara tashe a banan, da Garzali Miko da Maryam Waziri.

Sabbin jarumai

Wani lamarin kuma shi ne yadda aka samu jarumai sababbi da suke jan fim da ba a yi tsammanin hakan ba a baya.

Daga ciki akwai Daddy Hikima wanda aka fi sani da Abale da yake fitowa a matsayin boss a fim, wanda a da ba kasafai irin wannan jarumi ke zan fim ba.

Haka kuma akwai Ummi Rahab da Momme Gombe da Aisha Izzar So da Rukky Alim da kuma Amina Rani, wadda tsohuwar matar Adam Zango ce da sauran jarumai sababbi da yanzu ake yi da su a masana’antar.

Wasu abubuwan murna da suka faru sun ha da haihuwar matar Adam Zango safiya da ta haifa masa ’ya mace da kai Hamza asibiti da kasa samun haxin kai da ake yi da sauransu.