✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Mun kama soja dumu-dumu yana ba ’yan ta’adda kaki da albarusai’

Gwamnatin ta ce an sami nasarar ne sakamakon bayanan sirri daga mazauna gari.

Gwamnatin Jihar Zamfara ta yi zargin cewa an kama wani jami’in soja tare da budurwarsa a kwanan nan bayan an same su da hannu dumu-dumu suna bayar da kakin sojoji da kuma albarusai ga yan bindiga a jihar.

Mataimkain Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Jihar, Bashir Muhammad Maru ne ya tabbatar da hakan yayin wata zantawa da ’yan jarida ranar Juma’a, inda ya ce an sami nasarar ne sakamakon bayanan sirri daga mazauna gari.

A cewarsa, “Yayin da gwamnati take jiran matakin da Rundunar Soja zata dauka akan wannan lamarin sannan ta fitar da matasayarta a hukumance, batun ya kara fito da maganar da Gwamna Matawalle ya sha yi a baya cewa matukar ba a kakkabe bata-gari da masu zagon kasa ba, ba lallai ne a cimma nasarar da ake sa ran gani a yaki da yan bindiga ba.

“Ina son yin amfani da wannan damar wajen jinjinawa mutumin da ya sami kwarin gwiwar zuwa ya fallasa wannan bayanin wanda ya kaimu ga kama wadanda ake zargin. Godiyarmu ba ta da iyaka,” inji shi.

Sai dai ya kuma karyata wasu rahotanni dake cewa an hallaka mutane 40 a wani hari da aka kai garin Tungar Baushe na jihar ranar Laraba.

Sai da wakilinmu ya tuntubi kakakin Rundunar Tsaro ta Operation Hadarin Daji a jihar Zamfara, Kaftin Ibrahim Yahaya ya ce har yanzu batun zargi ne kawai kuma binciken sojoji ne kawai zai tabbatar da gaskiya ko akasin hakan.

Ya ce gwamnatin jihar ba ta tuntubesu ba kafin ta fallasa batun ga yan jarida.