✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna bukatar karin kudade don yaki da barayi – Shugaban EFCC

Ya ce hukumar na bukatar kudin don yakar rashawa

Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), Abdulrashid Bawa, ya ce dole a kara wa hukumarsa kudade matukar ana so yakin da take yi da barayi ya sami nasara.

Ya bayyana hakan ne lokacin da ya bayyana a gaban Kwamitin Yaki da Rashawa na Majalisar Wakilai a ranar Talata.

Da yake zantawa da ’yan jarida bayan kammala zaman, Abdulrashid ya ce sun bukaci karin kudi don Makarantar Yaki da Rashawa ta hukumar da ma sauran ayyukanta na yau da kullum.

Ya ce, “Gaskiya ne muna gina sabuwar makarantar yaki da rashawa, kuma muna bukatar kudin kammala ta. A bara, an ware mata Naira biliyan uku, amma a bana ko sisi ba a ware ba.

“Wannan ne ya sa muke rokon ’yan majalisa saboda muna bukatar wannan makaranta saboda akwai kwasa-kwasan da muke son koyawa don yaki da wadannan miyagun. Hanyar kawai da za mu iya yin hakan kuma ita ce ta yawan ba da horo a kai a kai.”

Ya nuna kwarin gwiwarsa cewa Majalisar, wacce ya ce tana da kyakkyawar alaka da hukumarsa, za ta amince da bukatar tasu.

Shugaban ya kuma ce EFCC ta sami nasarar kwato dimbin kadarori daga barayi da dama.