✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna so DSS ta gayyaci Davido — MURIC

Kungiyar MURIC mai rajin kare hakkin Musulmi a Najeriya, ta yi kira ga Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS), da ta gayyaci mawaki David Adeleke, wanda…

Kungiyar MURIC mai rajin kare hakkin Musulmi a Najeriya, ta yi kira ga Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS), da ta gayyaci mawaki David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido.

MURIC ta yi wannan kira ne saboda wani bidiyo da mawakin ya wallafa, wanda al’ummar Musulmin suka yi Allah wadai da shi.

Aminiya ta ruwaito cewa Shugaban MURIC, Farfesa Ishaq Akintola ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin a Abuja.

A karshen makon da ya gabata, Davido ya wallafa bidiyon Logos Olori, wani sabon matashin mawaki, wanda ya nuna wasu mutane sanye da jallibiya suna sallah inda daga baya kuma suka bige da rawa a inda suka yi sallar.

Wannan lamarin ne dai Musulmi suka bayyana a matsayin batanci ga addininsu.

A bidiyon har ila yau, an ga Olori a cikin wakar tasa mai suna “Jaye Lo” wacce Davido ya wallafa, ya zauna a saman wani masallaci yana raye-raye.

“Muna masu jan hankalin jami’an DSS, da su gayyaci mutanen biyu (Davido da Olori) don amsa tambayoyi kan dalilinsu na yin wannan bidiyo da zai iya ta da fitina a Najeriya,” Farfesa Akintola ya ce.

MURIC har ila yau, ta yi kira ga hukumar da ke kula da kafafen watsa labarai ta NBC da ta tace fina-finai (NFVCB), da “su haramta wannan bidiyo na wakar ‘Jaye Lo’ da Logos Olori ya yi.”

Tuni dai Davido ya cire bidiyon a shafukansa na sada zumunta bayan da aka yi ta sukar shi a kafafen sada zumunta.

Daga cikin fitattun mutanen da suka soki Davido, akwai jarumin Kannywood Ali Nuhu da tsohon mai bai wa tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari shawara kan sha’anin kafafen sada zumunta, Bashir Ahmad.