✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutane 1,883 sun sake harbuwa da COVID-19 cikin sa’o’i 24 a Najeriya

NCDC ta bayyana hakan ne a shafinta na Intanet, a ranar Asabar.

Cibiyar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) ta tabbatar da mutane 1,883 sun sake kamuwa da COVID-19 a fadin Najeriya a rana daya.

Hakan dai ya kawo adadin masu dauke da cutar zuwa 130,557 ya zuwa ranar Asabar a fadin kasar.

NCDC ta bayyana hakan ne a shafinta na Intanet, a ranar Asabar.

Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya (NAN), ya rawaito cewa an yi wa mutane 1,270,523 gwajin cutar, tun bayan bullarta a ranar 27 ga Fabrairun 2020.

Hukumar Lafiya ta Kasa, ta tabbatar da rasuwar mutum daya cikin sa’o’i 24, wanda ya kawo adadin wanda suka mutu zuwa 1,578.

NCDC ta ce wanda suka sake harbuwa da cutar, mutane 1,883, sun fito ne daga jihohi 22 ciki har da Babban Birnin Tarayya, Abuja.