✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutanen da aka kashe a fadan Hausawa da ’yan kungiyar asiri sun karu

Ragowar mutanen na kwance a asibiti rai kwakwai, mutu kwakwai

Karin mutum daya ya sheka lahira daga cikin mutanen da rikicin Hausawa da ’yan kungiyar asiri ya ritsa da su, ragowar kuma na kwance rai kwakwai mutu kwakwai.

Mutane da dama ne suka samu munanan raunuka bayan ’yan kungiyar asirin sun far wa al’ummar Hausawa ’yan tireda, inda suka hallaka mutum daya nan take, sauran da aka jikkata kuma aka garzaya da su zuwa asibiti, a unguwar Sabo da ke Jihar Osun.

A ranar Asabar ce Karin mutum daya daga cikin wadanda ake jinya sakamkon rikicin na ranar Alhamis ya ce ga garinku nan.

Sarkin Hausawarn Sabo Osogba, Alhaji Lawal Gomina ya ce mutum na farko harbe shi ’yan kungiyar asirin suka yi, dayan kuma ya rasu ne sakamkon raunuka da suka ji masa.

Limamin Masallacin Isala Mosque da ke Osogbo, Malam Basir Muhammed ya ce an riga an binne wanda ya ranar Asabar, bisa tsarin Musulunci.

Malam Bashir ya akasarin wadanda ke asibiti ba su san ma inda suke ba.

Rikici ya barke a lokacin da ’yan kungiyar asiri da ke jana’izar daya daga cikinsu da ya mutu, suka yi karo a kan hanya da wasu matasa da ke yin shagulgula a yammacin Alhamis.

Limamin ya ce ’yan kungiyar asirin sun kai hari a unguwar Sabo, suka kona kadarori suka raunata mutane da dama kafin isowar jami’an tsaro.

Kakakin ’yan sanda na Jihar, Yemisi Opalola ta ce al’amura sun daidaita a Sabo, sai dai ta ke cewa uffan kan adadin mutanen da aka kashe.