✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Mutanen da suka mutu a ambaliyar Libya za su iya kai wa 20,000’

Magajin Garin Derna, inda aka samu ambaliyar ne ya sanar da hakan

Magajin Garin Derna, garin da aka samu ambaliyar ruwa a kasar Libya, Abdulmenam al-Ghaithi ya ce akwai fargabar yawan mutanen da suka mutu su kai tsakanin 18,000 zuwa 20,000.

Al-Ghaithi, ya shaida wa gidan talabijin na Al-Arabiya mallakin kasar Saudiyya cewa sun yi hasashen ne la’akari da yawan yankunan da ambaliyar ta shafa.

Mahukunta dai sun ce ya zuwa yanzu, adadin mutanen da suka bace sun kai 10,000.

Garin dai ya yi kaca-kaca da tsummokara da kayan wasan yara da katakwaye da takalma da sauran tarkacen da ruwan ya koro daga gidajen jama’a.

Bugu da kari, taɓo ya rurrufe tituna sannan ya haƙo bishiyoyi sannan ya lalata motoci, wasu da dama ta juya su, ƙasansu ya koma sama. Akwai ma motar da aka gani a saman wani bene mai hawa biyu.

Mazauna garin na Derna dai na cikin matsanancin bukatar agajin gaggawa yayin da ma’aikatan ceto ke ci gaba da kokarin zakulo gawarwaki daga cikin taɓo.

An fuskanci ambaliyar ce da daren Lahadi, a garin da yake gabar ruwa, wanda galibi yake zama a bushe. Dogayen gine-gine sun rufta da mutane a ciki lokacin da suke barci.