✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 3,200 sun amfana da zakkar miliyan N10 a Kazaure

Masarautar Kazaure ta ce an rana zakkar ce ga mabukata a tsakanin gundumomi tara a yankin

Masarautar Kazaure a Jihar Jigawa ta raba zakkar kudi ta Naira miliyan 10 ga marasa galihu 3,200 a yankin.

Mai magana da yawun masarautar, Malam Gambo Garba ne ya bayyana haka a tattaunawarsu da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ranar Juma’a a Dutse, babban birnin jihar.

Malamin ya ce an rabar da kudin ne ga wadanda suka cancanta a gundumomi tara da ke masarautar.

A cewar Garba, Shugaban Kwamitin Tara Zakka na Masarautar, Alhaji Bala Muhammad, ya ce, nan ba da dadewa ba za a fadada raba zakkar da aka tara zuwa ga majinyatan da ke asibitoci daban-daban a yankin Kazaure.

Garba ya kara da cewa, Sarkin Kazaure, Alhaji Najib Hussaini, ya ba da tabbacin masarautar za ta ci gaba da ba da himma wajen karba da kuma raba Zakkar kamar yadda addini ya tanadar.

(NAN)